Gwamnatin Jihar Kano ga ce Cutar Kwalara wacce aka fi sani da Amai da Gudawa ta kashe mutum biyar sannan ta kama wasu mutum 189 a Kananan Hukumomi 20 na jihar.
Kwamishinan lafiya na Jihar, Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata.
- Buhari ya bai wa Ministan Ilimi mako 2 ya kawo karshen yajin aikin ASUU
- LABARAN AMINIYA: An Kara Farashin Fetur Daga N165 A Najeriya
Tsanyawa, ya kuma ce mutum 184 daga cikin adadin sun warke, wanda hakan ya ayyana jihar a sahun gaba na masu yaki ta yaduwar annobar.
A cewarshi, Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta tattara alkaluma inda ta ayyana kamuwar mutum 2,339 da suka kamu da cutar a Jihohi 30 na kasar nan daga watan Janairu zuwa Yunin shekarar 2022.
“A shekarar da ta wuce, Jihar Kano ta samu mutum 12,116 da suka kamu da cutar Amai da Gudawa, yayin da 329 daga cikinsu suka mutu. Amma a wannan shekarar, an samu ci gaba, wanda yana da alaka da kokari da kuma ajiye matakan kariya da aka yi wajen dakile yaduwar annobar,” inji Kwamishinan.
Ya bayyana rashin tsafta a matsayin matakin farko da yake assasa cutar ta Amai da Gudawa a cikin al’umma.
Kwamishinan ya yi kira ga al’umma da su kula da tsaftar muhallinsu da ta abinci da kayan marmari da jikinsu domin kaucewa kamuwa da cutar, musamman a wannan yanayi na damuna.
Daga karshe ya jaddada kudiri da kokarin gwamnatin jihar wajen tabbatar da lafiyar al’umma.