Cutar Kwalara ta kashe akalla mutum 325 daga cikin mutum 14,343 da ta kama a Jihohi 16 na Najeriya da suka bayar da rahoton bullarta a cikin wata shida.
Alkaluman baya-bayannan daga Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) sun nuna cewa yawan Jihohin da suka kamu ya zuwa 27 ga watan Yuni sun hada da Binuwai da Delta da Zamfara da Gombe da Bayelsa da kuma Kogi.
- ’Yan sa kai za su fara jagorancin yaki da ’yan bindiga a Sakkwato – Tambuwal
- Kwalara ta yi ajalin mutum 60 a Abuja
Sauran sun hada da Sakkwato da Bauchi da Kano da Kaduna da Filato da Kebbi da Kuros Riba da Neja da Nasarawa da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
Rahoton ya kuma lura cewa an sami karuwar wadanda suka kamu da cutar a makonni biyu na karshen watan Yuni.
“Jihar Zamfara na da mutum 191, Bauchi na da 2,163, Kano 891, Kaduna 129, sai Filato mai 82 wadanda su ne kimanin kaso 95.2 cikin 100 na mutum 3,543 da suka kamu a makonni biyun,” inji rahoton.
Binciken Aminiya ya kuma gano cewa an sami karin yawan masu kamuwa da kuma masu mutuwa sanadiyyar cutar a ’yan kwanakin nan
A Abuja alal misali, yawan wadanda suka kamu ya kai 60, kamar yadda Minista a Ma’aikatar birnin, Ramatu Tijjani Aliyu ta sanar ranar Alhamis.
NCDC ta ce Kwalara wata annoba ce da wata kwayar cuta da ake kira da ‘vibrio cholera’ ke haddasawa, wacce ke da matukar hatsari ga rayuwar dan Adam kuma tana bin hanyoyin ruwa ne.
Galibi dai, an fi kamuwa da ita ne ta hanyar ci ko shan gurbataccen abinci ko ruwa, ko kuma ta’ammali da ruwan da ba tsaftatacce ba ne da kuma muhalli mai datti.
Wasu daga cikin alamomin cutar sun hada da amai da gudawa da kuma karewar ruwa a jiki, wanda kan iya haifar da matsala ga koda, ya haifar da suma, mutuwar nan take da kuma rashin karfin jiki.
Kazalika, cutar ta kan haifar da yawan jin kishi, rashin yin fitsari ko da batare da ciwon mara ba da kuma matsanancin zazzabi.
Likitoci sun ce ba lallai ne wanda ya kamu ya nuna alamu da zarar ya kamu da cutar ba, zai iya jimawa yana yawo da ita.
Yadda za a kare kai daga cutar
Kwararru a harkar lafiya sun ba da shawarar tabbatar da tsaftar jiki da ta muhalli a matsayin babbar hanyar kare kai daga kamuwa da cutar Kwalara.
Hakan ya kunshi wanke hannuwa a kai a kau da ruwa da sabulu.
Ita kuma tsaftar muhallin ta kunshi share magudanun ruwa da kuma tabbatar da cewa ruwan da mutum yake sha mai tsafta ne ta hanyar dafa shi ko kuma ta yin amfani da sinadaran tsaftace shi kafin a sha domin ya kashe kwayar cutar.
Bugu da kari, sun ba da shawarar cewa masu jinyar wadanda ke fama da amai da gudawa su tabbatar suna wanke hannuwansu a duk lokacin da suka taba tufafi ko fitsarin mai dauke da cutar.