✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Cutar COVID-19 za ta tsananta a 2021 —WHO

Tedros ya gargadi kasashen duniya kan yadda cutar za ta iya tsananta a shekarar 2021.

Hukumumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargadi cewar annobar COVID-19 za ta iya yin tsanani a shekarar 2021.

Shugaban Hukumar, Tedros Adhanom Ghebreysus, ya gargadi kasashe da su ci gaba da bin matakan kariya da kuma karbar rigakafin COVID-19 don dakile tasirinta.

Runi Bazuwar cutar ta kara kamari tuni a kasar Japan, inda aka fadada dokar kulle, yayin da wasu ke kira da a dage gasar Olympic da za a yi a kasar.

Hukumomin Japan sun fadada dokar kullen yankunan kasar uku, makonni 10 kafin fara gasar wasannin motsa jiki ta Olympic.

Masu adawa da gudanar da gasar suka mika wasikar neman soke ta, wadda mutum sama dubu 350,000 suka sanya wa hannu.

A yayin da Tokyo da sauran yankuna ke karkashin dokar kulle har zuwa karshen watan Mayu, Hiroshima, Okayama da Arewacin Hokkaido, inda za a gudanar da gasar Olympics ta tsere za su shiga layin inda za a kulle.