An samu karin mutum biyu da suka mutu a sakamakon cutar coronavirus a Najeriya kamar yadda Hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa a kasar NCDC ta bayyana.
Kididdigar alkaluman da NCDC ta fitar a ranar Lahadi, 18 ga watan Oktoba sun nuna cewa zuwa yanzu jimillar wadanda cutar ta kashe a fadin kasar sun kai 1,125 tun daga watan Fabrairun bana da ta bulla.
- Babu wanda cutar Coronavirus za ta kashe a jihata – Ishaku
- Waiwaye: Wata 6 bayan bullar cutar coronavirus a Najeriya
Haka kuma alkaluman sun nuna cewa an samu karin mutum 133 da cutar ta harba cikin jihohi 9 da suka hada da Legas(90), Ribas (13), Abuja (8), Kaduna (8), Oyo (6), Ondo (3), Katsina (2), Nasarawa (2), da kuma Filato (1).
Ya zuwa yanzu dai cutar ta harbi mutum 61,440 a fadin Najeriya yayin da aka sallami mutum 56,661 daga cibiyoyin killace masu cutar bayan sun samu waraka, sai kuma mutum 1125 da suka riga mu gidan gaskiya.