A shekaranjiya Laraba ne aka samu hoton da ya nuna shahararren dan kwallon Real Madrid kuma haifaffen Fotugal Cristiano Ronaldo ya rike wani kwalin da ya nuna yana goyon bayan Shugaba Goodluck Jonathan a zaben da za a yi a watan gobe.
Hoton ya nuna Ronaldo wanda shi ne Gwarzon dan kwallon duniya na bana rike da kwalin da ke dauke da sakon “Ina goyon bayan Jonathan a shekarar 2015”.
Sai dai bazuwar hoton ke da wuya a kafofin sadarwa musamman ta facebook da twitter da sauransu sai aka fara takaddamar sahihanci ko rashin sahihancin hoton. Yayin da wadansu ke ganin hoton ba gaskiya ba ne, an yi wani siddabaru ne wajen hada hoton wanda aka fi sani da Photoshop, wasu kuwa cewa suka yi hoton na gaskiya ne, babu wani siddabaru a ciki.
Wadanda suka gaskata hoton sun bayar da hujjar cewa, ganin yadda dan kwallon yake neman suna a fadin duniya ba abin mamaki ba ne don ya goya wa Jonathan baya. Wadansu kuwa cewa suka yi me ya hada biri da gada? ganin yadda babu abin da ya hada dan kwallon da siyasar Najeriya ballantana har ya goyi bayan wani shugaba a zaben da ke tafe.
Ko ma dai mene ne yanzu ya rage wa jama’a su yanke hukunci sahihancin ko rashin sahihancin hoton.