✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cristiano Ronaldo ya samu kyautar FIFA ta musamman

Ban taba tsammani zan karya wannan tarihi ba da aka kafa.

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA, ta bai wa dan wasan gaba na Manchester United, Cristiano Ronaldo kyauta ta musamman la’akari da bajintar da ya yi a duniyar kwallon kafa wanda ba a taba yin kamarsa ba.

Ronaldo mai shekara 36 ya lashe kyautar ce a The FIFA Best Awards 2021, wato bikin bayar da kyautar gwarazan da suka yi fice a harkar tamaula a shekarar 2021 wanda aka gudanar a birnin Zurich na kasar Switzerland.

FIFA ta ce ta karrama Ronaldo la’akari da ta tarihin da ya kafa na zura kwallayen da wani dan kwallo a da ko a yanzu bai a taba jefa adadinsu ba a fagen wasannin kasashe.

Ronaldo wanda babu tantama ba a taba samun wani dan kwallo mai jajircewarsa ba wajen ganin ya yi nasara a kan duk abin da ya sa gaba, ya karya tarihin zura kwallaye a wasannin kasashe na duniya lokacin da ya jefa wa kasarsa ta Portugal kwallaye biyu a ragar Jamhuriyar Ireland, inda a yanzu ya ci kwallo 115.

Ana iya tuna cewa a watan Satumbar bara ne Ronaldo ya kafa tarihi a matakin wasannin kasa da kasa bangaren maza, inda ya jefa kwallaye 115 a wasanni 184.

Wannan kyauta ta musamman da Ronaldo ya samu a bikin bayar da kyautattuka da FIFA ta gudanar, ita ce irinta ta farko da aka taba ba wa wani dan wasa da shakka babu wanda ya cancanta sai shi din.

A jawabinsa bayan hawa mumbarin karbar kyautar, Ronaldo ya yi godiya ga dukkan abokan tawagarsa, musamman ’yan wasan kasarsa da suka yi fadi-tashi tare a shekarar 2020.

“Ban taba tsammani zan karya wannan tarihi ba da aka kafa na kwallaye 109, amma sai ga shi na jefa kwallaye har 115.

“Har na zarta da kwallaye shida a kan tarihin da aka kafa na mafi yawan kwallayen da wani dan wasan ya ci wa kasarsa.

“Tabbas wannan abun alfahari ne a gare ni da har na samu wannan kyauta ta musamman daga Hukumar FIFA, wacce a kullum babu wani abu da nake ji a raina gareta sai dai karamci,” a cewar Ronaldo.

A halin yanzu dai Ronaldo ya jefa kwallaye fiye da 800 a tsawon shekarun da ya shafe yana haskawa a tamaula, kuma daga ciki 115 kasarsa ta Portugal ce ta amfana.