✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cristiano Ronaldo ya nuna bacin ransa a kan sayar da Di Maria da dabi Alonso

Shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid da ke Sifen kuma haifaffen Fotugal Cristiano Ronaldo ya nuna bacin ransa a kan yadda mahukunta kulon din…

Shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid da ke Sifen kuma haifaffen Fotugal Cristiano Ronaldo ya nuna bacin ransa a kan yadda mahukunta kulon din suke sayar da zaratan ’yan kwallonsu ba tare da la’akari da illar da hakan ke haifarwa kulob din ba musamman a kakar wasa ta bana.
dan kwallon, wanda a yanzu yake rike da kambun gwarzon dan kwallon duniya ya shaidawa kafar sardarwar wasanni ta Goal.com a ranar Litinin da ta wuce cewa sayar da zaratan ’yan kwallo da kulob din yake yi bai dace ba.  Hasalima shi ne yake shafar yadda kulob din yake yin kwallo a kakar wasa ta bana.
dan kwallon ya nuna bacin ransa ne ganin yadda kulob din ya sha kashi a wajen Real Sociedad a gasar rukunin La-Liga ta Sifen a ranar Lahadin da ta wuce da ci 4-2 duk da cewa Madrid ce ke kan gaba a wasan da ci 2-0 kafin Sociedad ta fanshe kuma ta lashe wasan da ci 4-2.
Ronaldo, wanda bai buga wasan ba saboda raunin da yake fama da shi a gwiwarsa, ya ce idan aka lura da yadda kulob din yake cefanar da zaratan ’yan kwallonsa kamar Di-Maria wanda ya koma kulob din Manchester United da ke Ingila da kuma dabi Alonso da ya canza sheka zuwa Bayern Munich da ke Jamus abu ne da sam bai dace ba.
Sai dai ya hori takwarorinsa da ke wasa a Madrid su zage damtse don ganin sun cigaba da samun nasara a sauran wasannin da suka rage a kakar wasa ta bana.
Idan za a tuna kulob din Madrid dai ya sayar da Angel Di-Maria ne ga kulob din Manchester United a makon jiya sannan ya sake sayar da dabi Alonso ga kulob din Bayern Munich da ke Jamus.  Sai dai kulob din ya maye gurbin ’yan kwallon ne da  Tony Kroos daga Bayern Munich da kuma James Rodriguez da ke kwallo a kulob din Monaco a Faransa.