Injiniyoyi a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi sun kirkiro wadansu na’urori da za su taimaka wajen jinyar cutar coronavirus da ta addabi duniya.
Na’urorin da jami’ar ta kirkira sun hada da na’urar wanke hannu mai sarrafa kanta da na’urar da ke taimaka wa mai cutar wajen yin numfashi (ventilators) mai sarrafa kanta wadda ke amfani da hasken rana.
Injiniyoyin sun kuma kirkiro wani akwati wanda likitoci da sauran ma’aikatan jinya da ke kula da majinyacin za su yi amfani da shi don kare kansu daga cutar ta hanyar sanya shi a kan majinyacin yadda zai rufe kansa da hancinsa da bakinsa.
Kana kuma sun kirkiri injin feshi wanda zai rika feshi wa duk wanda zai shiga cikin dakin jinyar ko kuma in zai fito daga dakin ta yadda ba zai kamu da cutar ba ko da a ce zai taba karfen da wanda yake dauke da cutar ya taba ne.
Sannan injiniyoyin sun samar da wata manhaja mai gano marar lafiya cikin hanzari.
Da yake nuna wa ’yan jarida na’urorin, Shugaban jami’ar ta ATBU, Farfesa Muhammad Ahmad Abdul’azeez, ya ce sashen bincike na jamiar ne ya gudanar da wannan bincike a kokarinsa na samo hanyoyin da za a taimaka wajen jinyar cututtuka kamar Zazzabin Lassa, da COVID-19 domin ganin an samar da na’urori masu inganci kuma marasa tsada da za su taimaka wajen kawar da wadannan cututtuka dake kashe al’umma.
Shugaban jami’ar ya ce sun yi amfani da kayan aiki da ake da su a nan jihar wajen samar da wadannan na’urori, “abin da ke nuni da cewa idan muka yi amfani da irin arzikin da Allah ya ba mu za a taimaka wa kasarmu sosai”.
Farfesa Abdul’azeez ya nuna farin cikinsa dangane da wannan nasara da jami’ar ta samu, yana cewa, “Injiniyoyinmu sun kirkiro na’urori guda hudu: ta farko ita ce na’urar da za ta tsaftace ka idan za ka shiga wajen ba tare da ka yi mu’amala da kowa ba.
“Shi wannan injin wanke hannun da kanshi zai wanke maka hannu da tsaftace ka, abin da kawai mutum zai yi zai je ne ya shiga ta cikinsa ya dan tsaya ba tare da ya taba komai ba cikin ’yan dakikoki injin da kansa zai wanke mutum da feshin ruwan wanke hannu sai mutum ya fita. Ta wannan injin an samu kariya sosai.
“Sai kuma na’urar da ke taimaka wa numfashi (ventilator) mai sarrafa kanta. Injiniyoyinmu sun yi amfani da kayan gida wajen hada wannan na’urar.
“Sannan sun kuma hada da na’urar da za ta rika killace marar lafiya kamar wani akwatin da za a sa a ka ya rufe baki da hancin mara lafiyar wanda zai kare masu yi wa mara lafiya jinya.
“Na hudu kuma jami’ar ta iya samar da manhajar da ke duba lafiyar mutum ko yana da cutar ko babu cikin sauki—wannan babbar nasara ce”, inji Farfesa Abdul’azeez.
Shugaban jami’ar ya bayyana karancin kudi a matsayin babban abin da ke yi musu tarnaki.
Ya kuma ce idan jihohi na da bukatar injiniyoyin jami’ar masu hazaka a shirye suke su samar da na’urorin da yawa cikjin sauki don dukkan kayayyakin da za a yi aikin da su akwai su a nan ba sai an je wani wuri ba.
Ya ce idan har gwamnatoci da hukumomin kula da lafiya suka rungumi wadannan na’urori da suka kera za a samu ci gaba sosai a fannin kiwon lafiya.
- COVID-19: ‘Adadin gwajin da ake yi bai isa ba’
- Coronavirus: ‘Yadda muke yi da ’yan uwanmu da suka kamu’
Jagoran injiniyoyin, Faisal Sani Bala Tanko, ya ce na’urar tsaftace jiki da hannu da suka samar mai sarrafa kanta za ta yi matukar taimaka wa jama’a a masallatai, kasuwanni, da majami’u, da sauran wuraren da ake samun cunkoson jama’a,
Ya ce na’urar taimaka wa majinyaci numfashi sun mata hikima sosai wajen hada ta ta yadda za ta rika aiki da hasken rana tare da sanya mata batiri, sannan na’urar killace numfashin marar lafiya sun yi hikima wajen tsara ta domin kare jami’ai da kuma wadanda suke kusa da wajen da ake jinyar marar lafiya domin hana yaduwar cutar ga wadanda suke masa jinya.
Injiniya Tanko ya ce, “Akwai inda likita zai sanya hannayensa ya duba marar lafiya, wannan abu kamar akwatine, aikinsa shi ne zai ke tare numfashin marar lafiya ba tare da ya cutar da wani ba. Kun ga an samu kariya daga ko wanne bangare, sai kuma manhajar duba marar lafiyar cikin hanzari da muka iya samarwa tare da taimakon wuraren gwaje-gwajen kimiyya na jami’armu”.