Yau ce ranar aiki ta farko tun bayan da wata doka da hukumomin kasar Habasha suka kafa ta hana yin hannu da taruwar jama’a ta fara aiki.
A karshen mako ne dai aka ayyana dokar ta-bacin da nufin hana yaduwar cutar coronavirus.
Shafin intanet na BBC Afirka ya ruwaito cewa da ma dai an hana tarukan mutane da yawa, an kuma rufe makarantu.
Kuma ko da yake tun makon jiya aka ayyana dokar sai ranar Asabar aka yi bayani a kan abubuwan da ta shafa.
Da farko dai dokar ta haramta duk wani taron mutane da ya haura mutum hudu sai dai idan ya zama lallai da tilas—shi ma wajibi ne sai an samu izini daga hukumomi. Sannan an haramta yin hannu.
’Ya’yan gidan Sarautar Saudiyya 150 sun kamu da Coronavirus
Yawan masu Coronavirus a duniya ya haura miliyan 1
Daga yanzu, a cewar dokar, wajibi ne duk wanda zai fita bainar jama’a ya sanya amawali—abin rufe baki da hanci.
Haka nan kuma an wajabta wa masu motocin haya rage yawan fasinjojin da za su dauka da rabi, yayin da gidajen abinci da otal-otal kuma ba za su zaunar da mutum fiye da uku ba a teburi guda.
Bugu da kari dokar ta haramta wa masu gidajen haya korar ’yan haya da kara kudin hayar.
Sannan an haramta wa kamfanoni da masu sana’ar da wasu ke aiki a karkashinsu su kori ma’aikata da sunan harka ta tsaya.
Duk wanda aka samu da laifin karya wannan doka ka iya zaman kaso na shekara uku.
Hukumomin kasar ta Habasha sun ce dakatar da komai a kasar wadda ita ce kasa ta biyu a yawan jama’a a Afirka abu ne da ka iya wahala, amma suna fatan wadannan matakai za su taimaka wajen takaita yaduwar cutar.
Shafin na BBC ya ruwaito cewa a Addis Ababa, babban birnin kasar, har yanzu ana iya ganin mutane fiye da hudu sun taru, kuma bas u saka amawalin ba; sannan kuma ba a kara yawan jami’an tsaron da ke sintiri a titunan birnin ba.