✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

COVID-19 ta na dab da zama tarihi – WHO

Sai dai ya ce duk da haka ba za a nade hannu a zauna ba

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce tsawon saura kiris duniya ta ga bayan cutar COVID-19.

Ya ce sati biyu ke nan da ake samu mafi karancin adadin wadanda suka kamu da cutar tun bayyanarta a shekarar 2019.

Shugaban ya bayyana hakan ne ga manema labarai ranar Laraba, inda ya yaba wa kasashen duniya kan kokarinsu da ya kai ga cim ma wannan nasara.

A cewarsa, “Idan ba mu yi amfani da wannan damar ba, to za a kuma samun yaduwar wasu nau’ukan da mace-mace da rashin tabbas.

“Mun samar da wasu dokoki guda shida da za su taimaka wa kasashen duniya kawar da cutar baki daya, har ma da wasu bala’o’i da za a iya samu nan gaba.”

Ya kuma bukaci kasashen da su ci gaba da allurar rigakafin wadanda ke da hatsarin kamuwa da ita tare da ci gaba da yi musu gwajinta.

Hukumar ta WHO ta yi gargadin yiwuwar sake bullar cutar nan gaba, don haka ta yi kira ga kasashen da su kula da samar da isassun kayan aiki da ma’aikatan lafiya.

Wata babbar jami’a a WHO din mai suna Maria Van Kerkhove ta ce: “Muna sa ran za a samu bullar ta a gaba, mai yuwuwa a lokuta daban-daban, kuma musamman nau’in Omicron”.

“Ita ma cutar Kyandar Biri na ja da baya sosai, amma akwai bukatar kasashe su ci gaba da yaki da ita ta hanyar gwaji da rigakafi,” inji ta.