Akalla likitoci 303 ne suka mutu a kasar Indonesia bayan harbuwa da cutar COVID-19, kamar yadda Kungiyar Likitocin kasar ta bayyana a ranar Alhamis.
Daga cikin adadin, 169 manyan likitoci ne, sai kananan guda 129, sai likitocin masu neman kwarewa guda biyar.
- COVID-19: Kotu ta bude babbar kasuwar Abuja bayan biyan tara
- COVID-19: Saudiyya ta ba da izinin kwashe ’yan kasashen waje
- Dan Najeriya ne ya kirkiro rigakafin COVID-19 a Amurka
- An kama masu sayar da jabun rigakafin COVID-19
Galibi dai tsofaffin likitocin da suka mutu bayan harbuwa da cutar sun fara ne daga shekaru 81 zuwa 85.
Mafiya karancin shekaru da suka mutu daga cikinsu su ne masu shekaru 28 zuwa 30, su ma kimanin mutane 11.
Watan Janairun 2021 shi ne watan da aka fi samun mace-macen likitocin inda mutum 57 suka mutu, adadin da ya haura wanda aka samu a watan Disambar 2020 mai likitoci 55.
Jerin yankunan da aka fi samun mace-macen sun hada da Java ta Gabas mai mutane 60, Jakarta guda 44, Java ta Tsakiya, 44, Java ta Yamma, 34, da kuma Arewacin Sumatra mai mutane 27.