✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

COVID-19 ta kama dan jarida da iyalansa

Dan jaridar ya harbu da cutar shi da iyalansa uku, bayan yi musu gwaji.

Editan Jaridar Eggon da ke Jihar Nasarawa, Matthew Kuju da  iyalansa mutum uku sun harbu da cutar COVID-19.

Editan ya bayyana a ranar Litinin cewa ya dauki iyalansa suka je yin gwajin cutar a garin Lafia, kuma sakamakon ya nuna suna dauke da ita.

Ya ce, “Kwanaki biyu bayan gwajin, sakamakon ya nuna ni da iyalina muna dauke da cutar COVID-19.

“Dukkaninmu babu wanda ya nuna wasu alamu na rashin lafiya, amma mun killace kanmu, sannan muna karbar magani,” cewar Kuju.

Ya shawarci jama’a da su dauki ragamar zuwa yin gwajin cutar, don sanin sakamakonsu.

Sannan ya shawarci mutane da su ci gaba da bin matakan kariyar COVID-19, kamar yadda masana harkar suka tanadar.