Cutar Coronavirus ta harbi karin mutum 505 a fadin Najeriya kamar yadda alkaluman Cibiyar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa ta kasa (NCDC) suka tabbatar.
NCDC ce ba da sanarwar hakan a shafinta na Intanet a safiyar Laraba, inda ta ce adadin wanda suka harbu da cutar ya karu zuwa 172,262.
Hakan na zuwa ne a yayin da sabon nau’in cutar COVID-19 na Delta ke ci gaba da yaduwa a fadin Najeriya.
A kan haka ne NCDC da Gwamnatin Najeriya suka ayyana cewa an wannan shi ne zagaye na uku da annobar ta barke a fadin kasar.
Reshen Cibiyar NCDC da ke Jihar Legas ya bayyana cewar mutum 237 ne suka kamu da cutar, yayin da 83 suka kamu a Ribas.
An samu karin mutum 45 a Oyo da 22 a Ondo da 18 a Kuros Riba. Sai Kaduna da mutum 13 inda kuma aka samu mutum goma sha uku-uku a Ogun da Gombe.
Haka kuma, an samu mutum takwas sabbin kamuwa a Abuja, bakwai a Ekiti, da shida Delta, sai Bayelsa mai mutum uku, da mutum biyu-biyu a Edo da Neja.
A cewar NCDC an samu rahoton mutuwar mutum uku, wanda hakan ya kawo adadin wanda suka mutu zuwa 2,163.
Sai dai an samu mutum 85 da suka warke daga cutar kuma aka sallame su daga cibiyoyin killace masu ita a fadin kasar nan.
NCDC ta ce jimullar mutum 165,122 ne suka warke daga cutar tun bayan barkewartwa a Najeriya.
Kazalika, NCDC ta bayyana adadin mutum miliyan 2.5 a matsayin wadanda aka yi wa gwajin cutar daga cikin mutum miliyan 200 da ke rayuwa a kasar nan.
Alkaluman na NCDC sun nuna cewa an yi wa kaso shida daga cikin dari na mutanen da ake yi wa gwajin cutar a kullum.