Gwamnatin Saudiyya ta ba wa jirage daga kasashen waje izinin su shigowa su kwashe ’yan kasashensu da suka makale a kasarta.
Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta Saudiyya ta ce izinin bai shafi jirage daga kasashen da ke fama da sabon nau’in cutar COVID-19 da aka gano ba.
- An cafke basarake a cikin ’yan bindiga a Neja
- An kashe basarake mako daya bayan garkuwa da shi a Neja
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 48, sun kashe 2 a Katsina
Kazalika ba a amince wa ma’aikata jiragen sama da suka sauka a Saudiyya su fito daga jirgen ba.
Saudiyya ta rufe sufurin jiragen sama gaba daya na tsawon mako guda ne a makon jiya saboda rashin samun bayani kan sabon nau’in na COVID-19.
Kasar ta yi hakan ne bayan Gwamnatin Birtaniiya ta saka dokar hana fita a birnin London da yankin Kudu maso Gabashin Ingila don dakile cutar mai saurin bazuwa.