Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), ta sanar da bullar nau’in Omicron na cutar COVID-19 a kasashe 38 a fadin duniya.
Daraktar Hukumar, Dokta Maria Van Kerkhove, ita ce ta sanar da hakan a ranar Juma’a, inda ta ce cutar ta karade nahiyoyin duniya guda shida.
Ta ce za a dauki makwanni kafin a fahimci illar kwayar cutar ta Omicron da samo mata magani da kuma yadda za a kula da wadanda suka harbu da shi.
Har wa yau, ta ce tuni masana a fadin duniya suka dukufa don samar da mafita game da sabon nau’in kwayar cutar.
Shi ma a nasa jawabin, kakakin WHO, Richard Kenney, ya ce nan ba da jimawa ba za a samar da amsoshin tambayoyin da mutane ke yi game da Omicron.
Van Kerkhove ta kara da cewa ana zargin kwayar cutar Omicron na saurin yaduwa a tsakanin al’umma, amma za a dauki kwanaki kafin samun cikakken bayani game da hakan.
WHO ta bukaci jama’a da su ci gaba da karbar allurar rigakafin da ake bayarwa domin kare lafiyarsu da kuma sauran jama’a.