Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta amince da rigakafin cutar COVID-19 na kamfanin Pfizer.
Darakta-Janar ta NAFDAC, ta bayyana a Legas, ranar Juma’a cewa Hukumar ta amince da yin amfani da rigakafin kamfanin a Najeriya a matakin gaggawa.
- Hattara dai mata: Mu yi wa kanmu fada kafin ranar da-na-sani
- Batanci ga Sahabbai: An dakatar da malami daga yin wa’azi a Bauchi
- An kama barawon da ya sace wayar salula 247 a Katsina
- Azumin Bana: ‘Da kyar muke samun abinci’
Sahalewar rigakafin Pfizer na zuwa ne watanni kadan bayan NAFDAC ta ba da izinin yin rigakaficin cutar COVID-19 na Oxford-Astrazeneca a Najeriya.
Kawo yanzu, mutum miliyan 1.19 ne aka yi wa rigakafin cutar ta COVID-19 a Najeriya.
Hukumar Kula da lafiya a matakin farko ce ke sanya ido kan gudanar da allurar rigakafin cutar cikin aminci a madadin Gwamnatin Tarayya.