✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

COVID-19 na namen yada kyanda da shan-inna a Najeriya

Miliyoyin kananan yara a Najeriya na fuskantar barazanar kamuwa kyanda da shan-inna

Miliyoyin kananan yara a Najeriya na fuskantar barazanar kamuwa da kyanda, shan-inna da sauran cututtuka sakamakon tasgaron da dokar kulle ta kawo a kokarin yaki da annobar COVID-19.

Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin tsare-tsaren allurar rigakafin da aka saba gudanarwa, ko dai an jingine su ko kuma an dage su saboda annobar COVID-19.

Tasgaron na iya yin barazana ga nasarar da aka samu kan yaki da cutar shan-inna a Najeriya, wata daya bayan da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ba kasar shaidar fatattakar cutar.

– WHO da UNICEF na harsashen abubuwa ka iya dagulewa –

To sai dai WHO da Asusun Kula da Kananan Yara Na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) sun yi gargadin cewa tsaikon rigakafin na iya mayar da hannun agogo baya.

A cewar hukumomin biyu, “Ma’aikatan lafiya da dama ba su iya kaiwa ga wurare da dama ba saboda takaita zirga-zirga, mayar da su aikin yaki da COVID-19 ko kuma karancin kayan kariya”.

Dakta Aminu Magashi, wani kwararren likita da ke aiki da wata kungiya mai zaman kanta mai suna Africa Budget Health Network ya ce cutar ta kawo wa ayyukan rigakafi da dama tsaiko saboda ma’aikatan lafiya da dama na tsoron rashin isassun kayan kariya na iya jefa su cikin hatsari.

Ya ce rashin rigakafin ka iya jefa miliyoyin yara cikin barazanar kamuwa da kyanda da ma wasu cututtukan.

“Yara da yawa za su iya kamuwa da ciwon sanyi alal misali, ko amai da gudawa, duk wadannan cututtuka ne da za su iya hallaka su cikin gaggawa,” inji shi.

– Iyaye sun fara zaman dar-dar –

Tsawon lokaci dai ana jinjina wa iyaye musamman mata kan gudunmawar da suke bayarwa wajen yaki da cututtukan da su ke addabar kananan yara.

To sai dai da zuwan annobar coronavirus a Najeriya da sauran sassan nahiyar Afirka, iyaye da dama suka fara shiga halin zaman dar-dar.

“Lokacin da na ga yadda annobar coronavirus ke yin illa a kasashe tare da hallaka mutane, tsoro ya kama ni matuka ta yadda fita daga gida ma ya fara yi min wahala”, inji Hajiya Halima Sani, wata uwa mai ’ya’ya hudu a Kano.

Ta ce, “Tsoron kamuwa da cutar ya sa na ki kai ‘yata Surayya asibiti domin rigakafi, amma yanzu da abubuwa suka fara daidaita ina fatan kaita”.

Ita ma Misis Yinka Banjo ta ce tsoron kamuwa da cutar ya hana ta kai yaranta rigakafin wata shida da wata tara don kada malaman lafiya su shafa musu cutar.

“Amma tun da yanzu abubuwa sun fara sauki, zan kai yaran asibiti in musu bayani ko za a yi musu ta wata shida da ta shekara daya”, inji Misis Yinka.

Hajja Amina wata ‘yar gudun hijira daga Marte da ke zaune da ‘yan uwanta a yankin Gwange na Maiduguri a Jihar Borno, ta ce  ma’aikatan lafiya da dama na kaffa-kaffa da mata masu shayarwa saboda tsoron kamuwa da cutar.

– ‘COVID-19 ta hana mutane samun kulawar lafiya’ –

Babban Darakta a Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Kasa (NPHCDA), Dakta Faisal Shuaib ya ce annobar corona ta shafi dukkan ayyukan kula da lafiya a matakin farko ciki har da bangaren alluran rigakafi.

“Mun fuskanci yanayi da dama da dokar kulle ta hana mutane samun kulawar lafiya”, inji Dakta Faisal.

Shi kuwa Daraktan Sashen Dakile Yaduwar Cututtuka da Rigakafi na NPHCDA, Dakta Bassey Bassey Okposen, cewa ya yi akwai kokarin da suke yi na ci gaba da ayyuka a dukkan cibiyoyin lafiya.

Ya ce, “Shirye-shirye sun yi nisa wajen ganin dukkannin wadanda ba a yi musu rigakafin ba da ma wadanda suka rasa an yi musu”.