Hukumar Kawar da Zazzabin Cizon Sauro (NMEP) ta yi gargadi cewar za a mutuwar masu cutar a Najeriya da wasu kasashen Afurka za ta ninku a karshen 2020, in har aka kara rage magance ta.
Shugaban hukumar, Dakta Audu Bala Mohammed, ya bayyana haka a lokacin da yake magana da ‘yan jarida a Abuja.
Ya ce, wani bincike da kungiyar Global Fund ta yi ya nuna an rage kula da zazzabi da sauran wadansu ayyuka saboda mayar da hankali da kasashe ke yi wajen shawo kan annobar COVID-19.
Ya ce binciken ya gano hanyoyin kariya da dama da aka soke.
“Hasashen da aka yi kwanan nan ya ba da hasken cewar idan aka tsayar ko aka yi tsaikon bayar da kula da kariya na abubuwa kamar: Gidan sauro, magunguna ga masu juna biyu da sauransu, mutuwa ka iya ninkuwa a kasashen Saharar Afirka a wannan shekara.”
Ya ce, “inda binciken ya fi ban tsoro shi ne, yawan wadanda za su mutu sakamakon zazzabi a kasashen da ke yankin Saharar Afirka a 2020 sai ya fi yawan wadanda zazzabi ya kashe a duniya cikin shekarar 2000″.
Bala ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da kasashen da ke fama zazzabin cizon sauro da su daina tsayar da kariya ga cutar saboda yin hakan zai haifar da rasa rayuka da dama.
“Mu dai za mu ci gaba da samar da gidan sauro da raba magunguna da yin gwaji da sauran hanyoyin kariya”, inji shi
Ya ba da tabbacin cewar kungiyarsu za ta ci gaba da tsare-tsare hanyoyin magance yaduwar zazzabi har zuwa karshen shekara.
Sa’annan ya yi kira ga mutane da su ribanci hanyoyin kare Kansu daga cutar ta hanyar yin amfani da gidan sauro da shan maganin zazzabi ga masu juna biyu da kuma tabbatar da an ba yara ‘yan kasa da shekara biyar maganin zazzabi a lokacin rigakafi.