A kasar New Zealand, akalla mutum uku ne aka ba da rahoton mutuwarsu sanadiyyar daskarewar jini bayan sun karbi rigakafin COVID-19 na kamfanin Pfizer.
Hukumar Kula da Ingancin Allurar Rigakafin COVID-19 ta Kasar ce ta sanar da hakan ranar Litinin, inda ta ce mutanen sun mutu ne sakamakon matsalar, bayan an yi musu allurar rigakafin.
- Isra’ila ta haramta wa Yahudawa zuwa Amurka saboda Omicron
- Muhimman abubuwa a rikicin Tigray na kasar Habasha
“Hukumar ta zauna don tattauna korafe-korafen da ake samu don a gano ko suna da alaka da rigakafin ko kuma a’a,” inji sanarwar.
Mutanen da suka mutu dai sun hada da wani yaro mai shekara 13, da wani matashi mai shekara 26, da kuma wani tsoho mai kimanin shekara 60.
Sai dai hukumar ta ce ya zuwa yanzu ba ta kai ga gano alaka tsakanin allurar da daskarewar jinin a jikin tsohon mai shekara 60 ba, sannan tana bukatar karin bayani domin tantance rawar da rigakafin ta taka a mutuwar yaron mai shekara 13.
“Amma bisa ga bayanan da muka tattara, mun gano cewa daskarewar jinin ta faru ne a jikin wannan matashin mai shekara 26 sakamakon rigakafin,” inji sanarwar.
Rahotanni dai sun ce matashin ya fara nuna alamun cutar ne ’yan kwanaki kadan da yi masa rigakafin, sannan ya mutu cikin mako biyu da karbar zagaye na farko na allurar.
Hukumar dai ta amince cewa matsalar ta daskarewar jini na daga cikin illolin da aka fi fuskanta daga rigakafin na Pfizer, amma ta ce ita kanta COVID-19 din na iya haifar da matsalar daskarewar jinin.
Sai dai ta ce amfaninta ya zarce illolin da take da shi. (NAN)