✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Mutum 27 sun rasu, 56 na karbar magani a Nasarawa

Gwamnan ya shawarci mutanen jihar kan ci gaba da kiyaye matakan kariyar cutar.

Gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule ya ce mutum 27 sun rasu sakamakon kamuwa da cutar COVID-19, 56 kuma sun kara harbuwa, sannan an sallami 743 a Jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi yayin zaman Majalisar Zartarwar Jihar.

“Mutum 27 sun rasu, 56 na karba magani sannan 1,496 kuma sun sake harbuwa da cutar daga cikin mutum 15,023 da aka yi wa gwaji.

“Kananan hukumomin Lafiya, Keffi da Karu ne aka fi samun wadanda suka kamu da cutar COVID-19,” kamar yadda ya bayyana.

Gwamnan ya shawarci mutanen jihar da su ci gaba da bin matakan kariya daga COVID-19 don taimaka wa gwamnati wajen yaki da ita.

Sannan ya ja hankalin su kan yadda cutar ke kara yaduwa a tsakanin al’umma tun bayan sake bullarta a karo na biyu.

Gwamna Sule ya ce abin da ya sa ake kara samun masu cutar shi ne yadda gwamnatin jihar ta jajirce wajen gwajin cutar a Jihar.