Aƙalla mutum biyar ne suka mutu sakamakon ɓarkewar cutar amai da gudawa a Jihar Legas.
Kwamishinan lafiya na jihar, Farfesa Akin Abayomi ne, ya bayyana hakan, inda ya ce mutane 60 ne suka kamu da cutar.
- Sallah: Aminu Ado ya gayyaci hakimai hawan sallah
- Sallah: Gwamnatin Nasarawa za ta biya albashin watan Yuni
Ya ce, an samu ɓullar cutar da ke da alaƙa da cin abinci mara kyau da gurɓataccen ruwan sha a ungwannin da ke kewayen Eti Osa da Lagos Island, Ikorodu da ƙananan hukumomin Kosofe.
Amma tuni gwamnatin jihar ta ɗauki matakan kariya, inda ya buƙaci mazauna yankin da su yi taka-tsan-tsan tare da ɗaukar matakan hana yaɗuwar cutar amai da gudawa a jihar.
“Mun ɗauki matakan da suka dace a duk faɗin jihar. Don a sanar da hukumar kula da muhalli ta ma’aikatar lafiya da kuma hukumar kare muhalli ta Jihar Legas (LASEPA), domin gudanar da bincike kan wata majiya mai tushe da za ta iya gurɓata ruwa a yankin Lekki Victoria.
“Muna zargin yiwuwar ɓullar cutar amai da gudawa; duk da haka, an ɗauki samfurin gwaji don tabbatarwa.
“Ya zuwa ranar 28 ga watan Afrilu, 2024, Najeriya ta bayar da rahoton mutane 815 ake zargin sun kamu da cutar amai da gudawa da kuma mutuwar mutane 14 a jihohi 25,” in ji shi.