Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta sanar da mutuwar mutum biyu a ranar Alhamis sakamakon kamuwa da cutar COVID-19 a Najeriya.
Hakan dai ya kawo yawan wadanda suka mutu zuwa 2,742.
- Ba mu da shirin dawo da SARS —Shugaban ’Yan Sanda
- ’Yan sanda sun kwato mutum 187 daga hannun ’yan bindigar Zamfara
NCDC ta fitar da alkaluman ne a shafinta na intanet da safiyar ranar Juma’a.
Kazalika, hukumar ta ce akwai karin mutum 290 da suka kamu da cutar a Jihohi 14, ciki har da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Alkaluman na nuna cewa an sami ragin mutum bakwai daga cikin 297 din da suka kamu ranar Talata, kamar yadda NCDC ta bayyana.
NCDC ta bayyana cewar Abuja ce ke kan gaba da mutum 127 da suka kamu, yayin da Jihar Legas ke biya mata baya da mutum 45, Kaduna kuma na da mutum 28.
Sai kuma Jihohin Kudu maso Kudu na Delta da Ribas da Edo da Akwa Ibom ke da mutum 18, 10, uku da kuma mutum daya da suka harbu.
Jihar Kwara na da mutum 17, Filato 13, yayin da Jihar Nasarawa ke da mutum hudu da suka kamu.
A Zamfara kuwa, mutum 10 ne suka kamu, Imo na da mutum shida, Ekiti, Ondo da Oyo na da mutum biyar kowanensu.
Hukumar dai ta jadadda muhimmancin kiyaye matakan kariyar cutar da suka hada da sanya takunkumi, wanke hannuwa da kuma bayar da tazara.