Majalisar Dokokin Jihar Gombe ta bai wa gwamnan jihar shawarar da a rufe jihar na tsawon makwanni biyu.
Shugaban Majalisar Ibrahim Sadiq Kurba ne ya bayyana hakan a lokacin zaman majalisar na ranar Talata wanda aka yi sakamakon bullar cutar coronavirus a jihar.
Shugaban Majalisar ya ce ranar Talata da yamma zai gana da gwamna Inuwa Yahaya, ya shaida masa cewa tun da an samu bullar cutar har mutum biyar to a dauki wannan mataki.
Har ila yau dukkan ‘yan majalisar sun amince cewa duk wanda aka kama ya karya dokar shigowa Gombe daga wata jiha a killace shi na tsawon mako guda a sansanin ‘yan yi wa kasa hidima dake garin Amada a karamar hukumar Akko.
Kurba ya yi kira ga gwamnati da dauki kwakkwaran mataki a kan duk wani jami’in tsaro da aka kama yana sakaci da aiki wajen barin mutane suna shiga da fita daga jihar.
A daren Litinin ne dai Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa an tabbatar mutane biyar sun kamu da cutar coronavirus a jihar ta Gombe.