✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Ma’aikatan lafiya 53 sun harbu a Edo

Bayan sake bullar cutar a karo na biyu, mutum 244 sun kamu, 53 daga ciki ma'aikatan lafiya ne.

Ma’aikatan lafiya 53 ne suka harbu da cutar coronavirus a Jihar Edo, bayan sake bullarta a karo na biyu.

Shugaban kwamitin yaki cutar a Jihar, Dokta Andrew Obi ne ya bayyana hakan, inda ya ce an samu karin mutum takwas da suka kamu da ita, sannan mutum daya ya rasu a ranar Alhamis.

“Daga cikin mutum 240 da aka yi wa gwajin cutar, mun samu mutum takwas dauke da ita, sai mutum daya da ya rasu. Yanzu haka muna da mutane 238 da suka kamu da coronavirus.

“Bayan sake bullar cutar a karo na biyu, mun samu mutum 244 masu dauke da cutar, 53 daga ciki ma’aikatan lafiya ne.

“Mutum 202 sun warke, sai mutum 12 da suka rasu,” inji Obi.

Ya kara da cewa kwamitin zai bijiro da wasu sabbin hanyoyin sadarwa, don dakile yawaitar kamuwa da cutar a fadin jihar ta Edo.

Sannan ya ja hankalin al’ummar jihar game da amfani da takunkumi, wanke hannu karkashin ruwa mai gudana, rage shiga cunkoso da kuma wanke hannu da sinadarin tsaftace hannaye.