An samu karin mutum biyar da suka kamu da cutar coronavirus a kananan hukumomin Dutse da Auyo da Miga da Gwaram a jihar Jigawa.
Kwamashinan lafiya na jihar Dokta Abba Zakari Umar, ne ya tabbatar da hakan, yana cewa mutum biyu aka gano suna dauke da cutar ne a Dutse, mutum daya a Miga da mutum daya a Gwaram sai kuma mutum daya a garin Auyo.
“Yanzu haka a jihar Jigawa akwai mutum tara da suka kamu da cutar, amma mutum daya daga cikinsu ya rasu a karamar hukumar Dutse.” Inji Kwamishinan.
Kwamashinan, ya kara da cewa an dauki matakin rufe kananan hukumomin da abin ya shafa daga karfe 12 na daren ranar Juma’a mai zuwa.
- Coronavirus: An rufe garuruwa uku a Jigawa
- Coronavirus: Karin mutum 196 sun kamu a Najeriya
- Coronavirus: Jigawa ta karbi almajirai 524 daga Kano
Ya kuma ce, an umarci al’ummomin kananan hukumomin su tanadi kayan abinci don ganin ba a samu wata matsala ba.
Dokta Umar, ya kara da cewa tuni gwamnatin jihar ta dauki matakin raba kayan abinci da kudi ga wadanda aka hana fita domin a ragewa al’umma radadin da za su iya fadawa ciki.
Ko a ranar Talata ma dai gwamnatin ta Jigawa ta kafa dokar hana fita a garuruwa uku na jihar bayan da aka samu wasu mutane sun kamu da cutar.