✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yanke wa mutum 4 ɗaurin rai-da-rai a Jigawa

Kotun ta ce lauyan masu ƙara ya gamsar da ita da hujjojin da ya gabatar wanda babu shakka a kansu.

Wata Babbar Kotu ta yanke wa mutum huɗu hukuncin ɗaurin rai da rai bayan samunsu da laifin yi wa ’yar shekara 14 fyaɗe a unguwar Kurmi da ke Ƙaramar Hukumar Gwaram a Jihar Jigawa.

Waɗanda aka yanke wa hukuncin sun haɗa da Sale Ibrahim mai shekara 40, Amadu Saleh mai shekara 46, Sale Ali mai shekara 40, da Danlami Yusuf mai shekara 37.

Lauyan masu ƙara ya gabatar da shaidu huɗu da suka haɗa da rahoton likita tare da gabatar da shaidu guda biyu don tabbatar da tuhumar da yake yi wa ababen zargin.

Bayan sauraron dukkan ɓangarorin biyu a shari’ar, kotun ta ce lauyan masu ƙara ya gamsar da kotun da hujjojin da ya gabatar wanda babu shakka a kansu.

Dangane da hakan ne kotun ta samu waɗanda ake tuhuma da laifin fyaɗe wanda ya saba wa sashe na 3 (1) da kuma hukuncin da ya dace a ƙarƙashin sashe na 3 na dokokin Jihar Jigawa

Idan ba a manta ba, a kwanakin baya ne babbar kotun jihar ta yanke wa wani mutum, Aminu Ali mai shekara 25 hukuncin ɗaurin rai da rai bisa samunsa da laifin aikata fyaɗe da luwaɗi.