Gwamnatin Osun ta fara rabon buhunan shinkafa dubu arba’in da 333 ga jama’ar jihar domin saukaka musu radadin annobar COVID-19.
Wadanda za su samu tallafin sun hada da marasa galiyu, nakasassu, tsofaffin ma’aikata, malaman addinin Musulunci da na Kirista, da kuma maza da mata.
- An gano mai dauke da Coronavirus da ta gudu a jihar Osun
- An ba wadanda suka saci kayan tallafin Osun sa’o’i 72 su dawo da su
Shugaban Kwamitin Sanya Ido a kan rabon tallafin, Mista Ademola Adebisi, a ranar Alhamis, ya ce Gwamnatin Jihar ta yi tsari da yadda kowane bangare a jihar zai ci moriyar tallafin.
Ya kara da nuna farin cikinsa na ganin yadda rabon kayan tallafin ke tafiya bisa tsari.
A cewarsa tsarin da aka bi wajen rabon kayan tallafin zai tabbatar da cewar kowane bangare ko yanki na jihar ya samu na rabonsa.