Fitaccen jarumin masana’antar fina-finai Hausa ta Kannywood kuma mawaki, Sani Musa Danja, ya gargadi matasan Najeriya da su yi watsi da batun karyata annobar cutar COVID-19.
Sani Danja, wanda kuma yake wasan kwaikwayo da masana’antar fina-finai ta Nollywood a kudancin Najeriya, a ranar Juma’a ya bayyanawa Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) cewa, yanzu lokaci ne da kowa zai gane gaskiyar bullar cutar coronavirus sannan za a iya bin umarnin jami’an lafiya.
“Wannan cutar gaskiya ce ganin yadda adadin masu cutar ke mutuwa kullum.
“Cutar Coronavirus a fili take, don haka mutane sai su tashi tsaye su yi abin da ya dace wajen yakar wannan annobar da ta addabi duniya,” in ji Sani Danja.
Danja, ya ce duk da yake gwamnati tana bakin kokarinta, amma akwai bukatar a yaki cutar fiye da yadda ake yi yanzu don kaucewa illar yaduwar cutar da ceto rayuka.
“Idan kasashen da suka ci gaba irin su Amurka da suke da kayan kiwon lafiya na musammman, amma cutar na lakume rayuka ’yan kasar da yawa, Najeriya na bukatar ta yi da shiri muhimmi.”
- Yadda na yi jinyar coronavirus -Shugaban kwamitin COVID-19 na Kano
- Yadda na sha fama a killace har kwana 26 –El-Rufai
- Chloroquine na sha yayin jinyar coronavirus –Gwamnan Bauchi
“Akwai bukatar da gwamnati ta tanadi duk abin da ’yan kasar ke bukata, a wannan yanayi na kuncin rayuwa.”
“A nawa ra’ayin, gwamnati ta kara wa masu magungunan gargajiya karfin gwiwa don karin wata hanyar dakile cutar COVID-19.
“Wasu kashen sun gwada magungunan gargajiyan kuma ya yi masu aiki mai zai sa mu banbanta da su?”
Sani Danja, ya gargadin ’yan Najeriya da su daina yin siyasa da batun cutar COVID-19, sai dai a yi addu’ar annobar tazo karshen nan bada dadewa ba.
Jarumin wanda shi ne mamallaki kuma Daraktan sama da finanan Hausa 600 kadan daga ciki sun hada da; `Kwarya tabi Kwarya’ da ‘Jaheed, Nagari’ da ‘Wasiyya’ da ‘Harsashi’ da ‘Gidauniya’ da ‘Daham’ da ‘Jarida’da ‘Matashiya’ da ‘Zuga-zugi’da ‘Jan kunne’ da ‘Gambizam Raga’ da dai sauransu.
Sani Danja ya samu lambobin yabo a harkar fim da suka hada da: `The Awakening’, a wani fim na kare kai daga kamuwa daga cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV/AIDs wanda kasar Amurka ta dauki nauyi tare da Hukumar raya kasashe ta Amurka, USAID tare da gundunmawar hukumar lafiyar iyali ta duniya (Family Health International).