Daraktan sashin kula da na’urori da bunkasa su na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya Farfesa Muhammad Sani Sallau ya bayyana yadda jami’ar tayi kokarin kera na’urar taimakawa numfashi a wata zantawarsa da manema labarai a Zariya.
Ya ce, ayarin injiniyoyin jami’ar sun kera na’urar taimakawa numfashi da ba a kera irinsa ba a kasar nan, domin a cewarsa na’urar taimakawa numfashin da suka kera ya sha bamban da sauran kasancewar yana da wasu abubuwa da sauran basu da su.
Farfesa Sani Sallau wanda kuma shi ne shugaban riko na sashen kimiyyar kere-kere na jami’ar ya bayyana cewa,
injiniyoyin sun yi amfani ne da kayayyakin da suke da su a jami’ar domin kera ita wannan na’ura a matsayin gudunmuwarsu wajen yaki da cutar coronavirus a kasar nan.
Ya kara da cewa, ci gaba da jami’o’i ke da shi na gudanar da binciken kimiyya ne daga bisani masu masana’antu su sayi sakamakon binciken domin samar wa al’umma.
Daraktan ya bukaci gwamnati da ta samar da kudi domin kera na’urar da yawa ta yadda za a kaucewa sayo su daga kasashen waje domin yin amfani da su a gida.
”Cibiyar bunkasa binciken ma’adanai ta yi alkawarin hada jami’ar da kwamitin shugaban kasa akan yaki da cutar coronavirus don bayyana masu irin ci gaban da aka samu ko a samar da su da yawa a kasar nan.
Farfesa Sani Sallau ya yaba wa Injiniyoyin bisa jajircewar da suka yi domin ganin an sami nasarar kammala wannan gagarumin aikin duk da halin kulle da ake ciki.
Shima a nashi jawabin shugaban ayarin Injiniyoyin Dokta Kaisam Muhammad Usman na sashin kere-kere na jami’ar ta Ahmadu Bello ya ce makasudin kera wannan na’urar shi ne domin su tallafawa kokarin da gwamnati ke yi na yaki da annobar coronavirus a kasar nan.