Gwamnatin tarayya ta musanta labaran da ke yawo na cewa ta sake dawo da dokar kulle a fadin tarayyar kasar nan domin dakile bullar Coronavirus a karo na biyu.
Jagoran kwamitin Shugaban Kasa kan yaki da COVID-19, Dokta Sani Aliyu ne ya bayyana haka a cikin wani bidiyo da ya yi a ranar Alhamis.
- Kanin Sarkin Musulmi ya rasu
- Fintiri ya yi gargadi kan yaduwar coronavirus a zagaye na biyu
- Sanusi ya shawarci ’yan Najeriya a kan rigakafin cutar Coronavirus
- Tawagar WHO ta isa birnin Wuhan don gano asalin COVID-19
Dokta Sani Aliyu ya ce, “Muna sane da wani sako da ke yawo a kafafen sada zumunta cewar an dawo da dokar kulle, wannan ba gaskiya ba ne kuma ya kamata jama’a su yi watsi da shi.
“Ina rokon jama’a da su ci gaba da bin matakan kariyar COVID-19, ta hanyar amfani da takunkumi, rage shiga cunkoso da kuma wanke hannu.
“Muna da hanyoyin watsa labaranmu in har bukatar hakan ta sake tasowa; don haka a yi watsi da wancan sako da ke yawo a WhatsApp don ba gaskiya ba ne,” inji shi.
Ana iya tunawa Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta sanar a ranar Alhamis cewa a ranar Litinin 18 ga watan Janairun da muke ciki za a bude makarantu.
Hukumomin Najeriya na ci gaba da nuna damuwa kan yadda ‘yan kasar ke sabo dokokin kariyar cutar COVID-19 wadda yaduwarta a zagaye na biyu ya tashi hankalin kasashen duniya.
Zuwa yanzu dai sama da mutum 100,000 aka tabbatar da sun kamu da cutar a Najeriya, inda ta yi ajalin da dama daga cikin wadanda suka harbu da ita.