✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: ‘Gazawar’ Buhari wajen daukar mataki ta haifar da matsala

Gazawar Shugaba Muhammadu Buhari wajen daukar matakan da suka dace a kan lokaci ce ta sa cutar coronavirus ta yadu a wasu jihohin Najeriya, inji…

Gazawar Shugaba Muhammadu Buhari wajen daukar matakan da suka dace a kan lokaci ce ta sa cutar coronavirus ta yadu a wasu jihohin Najeriya, inji wasu masana.

A yanzu dai cutar ta bazu a jihohi 16 da Yankin Babban Birnin Tarayya, sannan akwai fargabar za ta ci gaba da yaduwa.

Masanan sun ce da shugaban kasar ya saurari shawarwarin wasu fitattun masana kimiyya tun lokacin da aka samu barkewar cutar a China, da yanzu Najeriya ba ta da wanda ya kamu ko kuma adadin wadanda suka kamu bai yi yawa ba.

Cutar ta bulla a karo na farko a Najeriya ne ranar 27 ga watan Fabrairu, kuma zuwa daren Laraba an samu mutum 276 da aka tabbatar sun kamu da cutar ta coronavirus saboda gwamnati ta gaza wajen bayar da umarnin rufe filayen jiragen sama da tashoshin ruwa da iyakokin kasa, tun bayan da aka samu rahoton bullar cutar a garin Wuhan na kasar China, kamar yadda masanan suka shaida wa Daily Trust.

Gargadin WHO

A ranar 30 ga watan Janairun 2020 ne Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana barkewar cutar COVID-19 a matsayin wata annoba da ya kamata duniya ta mayar da hankali a kanta.

Tun kafin nan, ranar 11 ga watan Janairun 2020, China ta sanar da mutuwar mutum na farko, wani mai shekara 61, sakamakon kamuwa da cutar bayan ya ziyarci  kasuwar dabbobi ta Wuhan.

Kwana 12 bayan nan, China ta fara daukar matakai masu tsauri nah ana shiga ko fita daga Wuhan, ta hanyar soke zirga-zirgar jiragen sama da na kasa da dakatar da duk wasu motocin sufuri na bas-bas da nufin hana yaduwar cutar a sauran yankunan kasar.

Ranar 11 ga watan Maris WHO ta sauya matsayin cutar COVID-19 daga annobar da ta addabi wani yanki zuwa annobar da ta addabi duk duniya, kuma ta yi kira ga kasashe da su binciko, su gwada, su kuma killace masu cutar, sannan su wayar da kan ’yan kasa ta yadda za a hana yaduwarta.

Tedros Adhanom Ghebreyesus
Darakta Janar na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) Dokta Tedros Adhanom Ghebreyesus (Hoto: Tesfanews)

An ce hukumar ta yi kiran ne saboda ganin yadda kasashe suka yi shakulatin bangaro ba su himmatu wajen daukar matakan gaggawa don hana cutar yaduwa ba.

Kuma duk da yadda cutar mai saurin kisa ke yaduwa kamar wutar daji a fadin Amurka daga China a tsakanin karshen watan Janairu da farkon watan Maris, gwamnatin Najeriya ta yi kunnen uwar shegu ga kiraye-kirayen a rufe filayen jiragen sama da tashoshin jiragen ruwa a matsayin wani mataki na kandagarki.

Haka ma yayin da kasashen Afirka kamar Kenya da Ghana suka yi zafin nama wajen rufe iyokokinsu tun kafin cutar ta yi yawa, Yaya Babba sai jan kafa take yi.

 Kiraye-kirayen masu ruwa da tsaki

Duk kiraye-kirayen da masu ruwa da tsaki irin su Kungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) da Kungiyar Masu Harhada Magunguna ta Najeriya (PSN) suka rika yi suna godn gwamnatin tarayya ta rufe iyakokin kasar ko a jikinta.

Misali, bayan an bayar da rahoton karuwar wadanda suka kamu a watan Maris, an ambato shugaban kungiyar NMA, Dokta Francis Faduyile, yana cewa lokaci ya yi da ya kamata gwamnati ta yanke shawarar “rufe iyakokinta ga kasashen da ke da masu cutar coronavirus da yawa”.

Wata kungiya mai zaman kanta ma wadda ake kira AIED ta yi kira ga Shugaba Buhari ya rufe iyakokin kasar.

Daraktan yada labarai na kungiyar, Kwamared O’Seun John, a wata sanarwa yake cewa, “Mun kasa fahimtar dalilin da ya sa gwamnatin Shugaba Buhari ta ki rufe iyakokin Najeriya, ta kuma ki rufe filayen jiragen samanmu da dukkan matafiya daga kasashen da coronavirus ta yiwa mamaya.

“Abu ne mai daure kai a ce mahaifi yana sane ko kuma da gangan zai tura ’ya’yansa cikin tarkon mutuwa don kawai ya nuna shi ya isa a yakin da ake yi da COVID-19 mai saurin kisa.

“Babu ko tantama Najeriya na daf da fuskantar barkewar cutar kamar Koriya ta Kudu, wadda ta dauki duk matakan da suka dace har zuwa lokacin da Majinyaciya ta 31 ta ki bin umarni nesanta kanta da jama’a….

“Wajibi ne Shugaba Buhari ya dauki mataki—wannan ba roko ba ne [domin kuwa] ya sha rantsuwar kare muradun Najeriya da ’yan Najeriy, don haka dole ne lafiyar ’yan Najeriya ta kasance gaba da komai”.

Zarge-zarge

Ba a jima ba kuwa gazawar shugaban kasar wajen amsa wadannan kiraye-kiraye na rufe iyakokin kasar ta tabbatar da zarge-zargen da ake yi cewa ya yi kunnen uwar shegu ne saboda yana sa ran dawowar ’yarshi daga Birtaniya.

Haka kuma an yi zargin cewa ya yi jinkirin rufe iyakokin ne saboda ya bai wa Shugaban Ma’aikatansa Abba Kyari wanda ke Jamus a lokacin da ma wasu manyan mutane da suka je wani bikin zagayowar ranar haihuwa London damar dawowa.

Daga bisani dai Malam Abba Kyari ya dawo kuma gwaji ya tabbatar da cewa ya kamu da cutar.

Ko da yake ranar 27 ga watan Fabrairu aka samu mutum na farko mai dauke da cutar a Najeriya, na biyu kuma ranar 9 ga watan Maris, sai bayan kusan wata guda, bayan wadanda suka kamu sun kai kusan 40, ranar 23 ga watan Maris, sannan kasar ta fara nuna alamun farfadowa da dogon barcin da take yi.

Malam Abba Kyari da Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi
Malam Abba Kyari yana hannu da Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi lokacin da ya jagoranci wata tawaga suka yi wa gwamnan ta’aziyya

Fargar jaji?

Ranar 18 ga watan Maris gwamnati ta ba da sanarwar hana matafiya daga China, da Italiya, da Iran, da Koriya ta Kudu, da Spaniya, da Japan, da Faransa, da Jamus, da Amurka, da Norway, da Birtaniya, da Switzerland, da Holand shogowa Najeriya.

A ranar ce kuma Ma’aikatar Lafiya ta bayyana samun karin mutum biyar da suka kamu da cutar ta COVID-19 a Najeriya.

Uku daga cikin mutanen daga Amurka suka zo, biyu kuma daga Birtaniya, a cewar Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa.

Kwana uku bayan nan, lokacin da gwamanti ke cewa za ta rufe manyan filayen jiragen sama biyu na kasar a biranen Legas da Abuja har tsawon wata guda, Ma’aikatar Lafiyar ta sanar da samun Karin mutum 10 da aka tabbatar sun kamu da coronavirus a Najeriya, lamarin da ya sa adadin ya kai 22.

Dukkan mutanen 10 kuma ’yan Najeriya ne, tara daga cikinsu daga cikinsu sun ziyarci Birtaniya da Spaniya da Holand da Canada da Faransa.

A cewar tsohon shugaban Kungiyar Masana kimiyya ta Najeriya, Farfesa Oyewale Tomori, yawan wadanda suka kamu da cutar zai karu saboda makara da Najeriya ta yi wajen daukar matakan da suka dace.

“A wata biyu na farko na abin da ya zama annoba ta duniya ba mu da wanda ya kamu ko daya, har ma kusan mun fara tunanin ba za ta kama mu ba, tunanin da rashin samunta a yankin kudu da Sahara na Afirka ya karfafa”, inji Farfesa Tomori.

Shi kuwa Sulaiman A. Sulaiman, Daraktan Cibiyar Bincike Kan Al’amuran Sadarwa da Yada Labarai a Jami’ar Amurka ta Yola, cewa ya yi ba kawai abin da gwamnatoci ke yi yanzu ko za su yi a makwanni ko watanni masu zuwa don hana cutar yaduwa ba ne abin ji, duk da muhimmancin da yin hakan ma ke da shi.

“Babban abin tambayar shi ne me ya sa ma aka bari cutar ta shigo Najeriya tun da farko? Wannan na da muhimmanci saboda koma dai yaya aka dubi lamarin, COVID-19 ba ta shigo Najeriya bisa larura ba, sai dai bisa gayyatar gwamnati.

“Gwamnati ta samu dama akalla sau uku ta hana cutar shigowa Najeriya, [amma] abin takaici ba ta yi amfani da ko daya daga cikinsu ba”.

Sannu ba ta hana zuwa

Bayan shiru na dogon lokaci sai a ranar 29 ga watan Maris Shugaba Buhari y aba da sanarwar hana fita a Legas, da yankin Babban Birnin Tarayya da jihar Ogun da nufin hana annobar yaduwa.

A cewar shugaban kasar, gwamnati za ta yi amfani da wannan dama don “ganowa, da bibiya, da kuma killace dukkan mutanen da suka yi mu’amala da wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar”.

Sai dai kuma yayin da mutane da dama ke yabawa da matakan da gwamnatin ta dauka don hana yaduwar cutar, wasu fargaba suka nuna cewa matakan ka iya taimaka mata ta karu.

Dokta Hussaini Majiya, shugaban Sashen Nazarin Kananan Halittu a Jami’ar Ibrahim Babangida da ke Lapai a jihar Neja, cewa ya yi wasu daga cikin matakan kamar dokar hana fita ko takaita hadahada da rarraba kayan abinci ko kudi da wasu jihohi ko ’yan siyasa ko masu hannu da shuni ke yi da nufin rage wa mutane radadin illar da zaman gida ka iya haifarwa alal hakika za su iya kara yada cutar.

Motsi ya fi labewa?

Sai dai kuma Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce tun bayan barkewar annobar a Najeriya ba ta zauna ba.

Darakta Janar na hukumar NCDC Chikwe Ihekweazu
Darakta Janar na hukumar NCDC Chikwe Ihekweazu

A cewar Darakta Janar na hukumar, Dokta Chikwe Ihekweazu, “Makwanni uku da gano mai dauke da COVID-19 na farko a China muka kafa cibiyoyin bincike a wurare biyar a Najeriya.

“A lokacin babu ko mutum guda da ya kamu a Najeriya….

“Yayin da aka samu karuwar masu dauke da cutar a mako guda da ya wuce, mun kara dakunan bincike guda biyu. A gaba daya muna da dakunan bincike guda takwas da za su iya gajin COVID-19 a Najeriya, kuma a watan gobe za mu kara wasu dakunan binciken shida”.

Ya kuma ce kasancewar babu allurar riga-kafin kamuwa da cutar, ya zama wajibi a dauki matakan kariya da suka hada da hana tarukan mutane da yawa da takaita zirga-zirga.