Gwamnatin China ta tallafa wa Najeriya da allurar rigakafin COVID-19 samfurin Sinopharm har kimanin 470,000.
Jakadan kasar a Najeriya, Cui Jianchun ne ya bayyana hakan ranar Juma’a, lokacin da ya ziyarci Ministan Lafiya, Osagie Ehanire a Abuja.
Ya ce ana sa ran allurorin rigakafin su karaso Najeriya nan ba da jimawa ba.
Mista Cui ya ce sun ba da tallafin ne don taimaka wa kokarin Najeriya na yaki da cutar COVID-19 da kuma yaukaka dankon dangantaka tsakanin kasashen biyu.
”Wannan kyakkyawan misali ne kan irin alaka me kyau da take tsakanin kasashen biyu,” inji shi.
Ministan Lafiya, Dokta Osagie Ehanire cewa ya yi Najeriya na maraba da tallafin, musamman kasancewar rigakafin kasar ya yanke tun ranar takwas ga watan Yulin 2021.
Ya ce kasar China na taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban Najeriya, yana mai cewa, “Wannan dangantaka ce mai kama da ta ’yan uwantaka, za mu ci gaba da ririta ta.”
“Bugu da kari, tallafin ba kawai zai taimaka mana ba ne wajen cike gibin da muke fama da shi a bangaren lafiya, har ma da sauran bangarori,” inji Ministan.
Tun daga watan Maris na 2021 zuwa yanzu, Najeriya ta yi wa kusan mutum miliyan hudu rigakafin COVID-19.