✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Babbar matsalar tattalin arzikin Najeriya

Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo ya ce Najeriya ta shiga tsaka mai wuya

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya ce Najeriya ba ta taba shiga matsin tattalin arziki a tarihinta ba irin na bana saboda annobar COVID-19.

Osinbajo ya ce sakamakon haka kudaden shigar kasar sun ragu da kusan rabi saboda faduwar farashin danyen mai da kuma kasancewar yawancin mutane yanzu ba su iya biyan haraji.

“Akwai lokacin da a watan Afrilu farashin tace danyen mai ya haura farashin da ake sayar da shi a kasuwa, ba wanda yake siya.

“Abun da nake cewa a takaice shi ne ‘yan watannin da suka gabata sun nuna mana gazawar dan-Adam wajen iya tsare-tsare, ballantana ya san abun da zai faru na gaba”, inji Osinbajo

Sai dai Osinbajo ya bayyana kwarin gwiwar cewa kasar da ma sauran kasashen duniyar za su farfado daga masassarar tattalin arzikin nan ba da jimawa ba.

Ya ce “Babu abun da bai girgiza ba sakamakon babban kalubalen da ya fada wa dan-Adam a wannan karnin.

“Mun shiga halin tsaka mai wuya, tattalin arzikin kasashe da dama ya shiga mawuyacin hali saboda wannan annobar.

“Amma ina da kwarin gwiwar cewa nan da wani dan lokaci da yardar Allah za mu ci galaba a kan wannan cutar”, inji shi