Gwamnatin jihar Kano ta bayar da sanarwar sanya dokar hana fita a fadin jihar na tsawon mako guda.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka a lokacin da ya yi wa jama’ar jihar jawabi.
Gwamnan ya ce dokar za ta fara aiki ne da karfe 10 na daren Alhamis.
- Yadda wayoyin salula ke ‘yada’ coronavirus
- Coronavirus: Majinyatan Kano ba su da alaka da juna
- COVID-19: A yi biyayya ga gwamnati —Masana
Ranar Talata ne dai Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta bayar da sanarwar samun karin mutum daya wanda ke dauke da cutar COVID-19.
Kwamishinan Lafiya Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya tabbatar da hakan.
Samun karin mutum daya da aka yi ya sa adadin mutanen da suka kamu a jihar ya kai hudu.
Ranar Asabar aka tabbatar da samu mutum na farko, wani jami’in diflomasiyya da ya yi ritaya, wanda aka ce ya yi tafiye-tafiye zuwa Legas, da Abuja, da Kaduna.