Adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da coronavirus a Najeriya ya karu da mutum 284, kamar yadda alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) na baya-bayan nan suka nuna.
Wannan adadi ne dai ya kawo jimillar wadanda suka kamu a kididdigar ta tsakar daren 20 ga watan Mayu a fadin kasar zuwa 6,677.
Daga cikin wannan adadi dai mutum 1,840 sun warke an sallame su, yayin da mutum 200 suka riga mu gidan gaskiya.
- Yadda aka samu sabanin alkaluma tsakanin NCDC da Zamfara
- Abubuwa bakwai da ba ku sani ba game da ayyukan NCDC
Sama da kashi biyu bisa uku na sabbin mainyatan dai, wato 199, a jihar Legas suke, yayin da wasu jihohin 11 da Yankin Babban Birnin Tarayya suka raba sauran a tsakaninsu.
Jihar Ribas ce ke kan gaba a cikin sauran da mutum 26, sannan jihar Oyo mai mutum 19.
Akwai kuma mutum takwas-takwas a Yankin Babban Birnin Tarayya da jihar Borno, mutum bakwai a Filato, shida a Jigawa, biyar a Kano, biyu a Abiya.
Jihohin Ekiti da Delta da Kwara da Taraba kuma na da mutum guda-guda.
A kididdigar jimillar wadanda aka tabbatar sun kamu, jihar Legas ta yi fintinkau da mutum 2,954, jihar Kano na rufa mata baya daga nesa da mutum 847, yayin da Yankin Babban Birnin Tarayya ke matsayi na uku da mutum 435.