An samu karin majinyata 338 a Najeriya, lamarin da ya kawo jimillar wadanda gwaji ya tabbatar sun kamu da COVID-19 a kasar zuwa 5,959.
Alkaluma na baya-bayan nan da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta wallafa a shafinta na Twitter sun nuna cewa daga cikin wannan adadi an sallami mutum 1,594 bayan sun warke, yayin da 182 suka riga mu gidan gaskiya.
Hukumar ta kuma kididdige sabbin majinyatan da aka samu a ko wacce jiha, kuma kididdigar ta nuna cewa 177 a jihar Legas suke.
A jihar Kano, kwana guda bayan alkaluman sun nuna babu wanda ya kamu, an samu mutum 64, yayin da aka samu 21 a Yankin Babban Birnin Tarayya.
Sauran jihohin su ne Ribas mai mutum 16, sai Filato mai 14, da Oyo mai mutum 11.
A jihar Katsina an samu mutum tara, hurhudu a Jigawa da Kaduna, uku-uku a Abiya da Bauchi da Borno, bibbiyu a Gombe da Akwa Ibom da Delta, sai kuma jihohin Ondo da Kebbi da Sakkwato masu guda-guda.
Jihar Legas ce dai ke da kaso mafi tsoka na wadanda suka kamu da mutum 2,550, sai jihar Kano na biye mata da 825, Yankin Babban Birnin Tarayya kuma na rufa musu baya da 418.