Gwamnatin Jihar Filato ta bayyana cewa an sallami mutum 10, da suke dauke da cutar coronavirus, bayan an yi masu gwajin cutar an tabbatar sun warke.
Kwamishinan lafiya na jihar Dokta Nimkong Lar wanda ke tare da sakataren gwamnatin jihar Farfesa Danladi Atu da Kwamishinan watsa labarai na jihar Mista Dan Manjang, ya bayyana cewa yanzu mutum 11 ne, suke jinyar cutar coronavirus a jihar.
Kwamishinan Lafiyan ya yiwa manema labarai karin bayanin ne a ranar Juma’a a garin Jos babban birnin jihar.
- COVID-19: ‘Plateau na bincike kan kwarmata sakamakon gwaji’
- COVID-19: Plateau na neman masu alaka da majinyaci na farko
“Mutum daya aka samu da wannan cutar a ranar Juma’a a Filato, sabanin bayanin mutum biyar da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta bayar. Domin daga baya hukumar ta sake gwada mutum hudu, kuma ta tabbatar cewa basu dauke da wannan cuta.”
‘’A cikin mutum 21 masu dauke da cutar coronavirus da muke da su a jihar nan. Mun sallami mutum 10, bayan da aka tabbatar yanzu basu dauke da wannan cuta, a gwajin da muka yi masu.
Don haka yanzu mutum 11 ne suka rage, wadanda suke dauke da wannan cuta a jihar nan. Kuma har ya zuwa wannan lokaci, babu wanda ya mutu sakamakon wannan cuta a jihar nan.’’