Gwamnatin Tarayya ta dakatar da matafiya daga kasashen Turkiyya da Brazil da Indiya daga shigowa Najeriya saboda karuwar masu kamuwa da cutar COVID-19 a kasashen.
Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan yaki da cutar a Najeriya, Boss Mustapha ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Lahadi.
- Zargin Batanci ga Annabi: An kai wa Kwamandan Kato-da-gora hari a Legas
- Sarkin Katsina ya dakatar da Hakimin Kankara
Boss Mustapha ya ce dakatarwara wacce za ta fara aiki ranar Talata za ta yi aiki ne na tsawon makonni hudu a karon farko.
Ya ce, “Mutanen da ba ’yan Najeriya ba da suka ziyarci kasashen Brazil ko Turkiyya ko Indiya a cikin kwanakin da suka gabaci sanya wannan dokar ba za a barsu su shigo Najeriya ba.
“Sai dai wannan matakin ba zai shafi wadanda kawai ya da zango suka yi a wadannan kasashen ba.
“Duk kamfanin jirgin da ya sake ya karya wannan dokar zai biya tarar Dala 3,500 a kan kowanne fasinja.
“Wadanda ba ’yan Najeriya ba ne suka yi yunkurin shigowa za a mayar da su kasashen da suka fito kuma kamfanin jirgin ne zai biya kudin jigilar tasu.
“’Yan Najeriya kuma da wadanda suke da takardar izinin zama ta dindindin za a tilasta musu killace kansu na tsawon kwanaki bakwai a cibiyar da gwamnati ta amince da ita ta killacewar, kuma sune za su dauki nauyin kansu,” inji sanarwar.
Har ila yau, sanarwar ta ce dole ne dukkan fasinjojin da suka shigo Najeriya daga wasu sassan su killace kansu na tsawon kwanaki bakwai sannan su je a sake yi musu gwaji bayan kwanakin sun cika.
Daga nan sai ya yi kira ga Gwamnatocin Jihohi da su taimaka wajen tabbatar da an bi wannan matakin sau da kafa.