Gwamnatin Jihar Osun ta ce ba za ta bude makarantu ranar hudu ga watan Janairun 2021 ba, sabanin sanarwar da ta bayar tun da farko.
Gwamnatin ta ce ta yanke shawarar ne saboda kaucewa barazanar dawsake bullar cutar coronavirus a karo na biyu.
- ’Yan bindiga sun bullo da sabon salon satar mutane
- ‘Na ga yadda ake horar da yara su zama ’yan bindiga’
- Boko Haram ta sace mata hudu a Adamawa
Mai ba gwamnan jihar shawara a kan harkokin ilimi, Alhaji Jamiu Olawumi ne ya bayyana haka da yammacin ranar Alhamis.
Ya ce, ma’aikatar ilimi ta Jihar na ta samun tambayoyi daga makarantun gwamnati da masu zaman kansu game da batun komawa makarantun a ranar da aka ayyana tun da fari a matsayin ranar komawa makarantun.
Jamiu ya ce sakamakon samun wasu dalilai da suke da alaka da sha’anin lafiya musamman masu alaka da annobar COVID-19, yasa gwamnatin Jihar yunkurin daukar matakan kariya a kai.
Ya ce, Ma’aikatar Ilimi ta jiha tare da takwararta ta lafiya za su yanke shawara su kuma fito da sabuwar sanarwar komawa makarantu a fadin jihar wanda sabuwar ranar gwamnati zata amince da ita sabanin sanarwar ta farko.
“Iyaye su sanya idanu akan ‘ya’yansu, su rarrashe su, ya kuma gargadi masu makarantu masu zaman kansu da su guji karya doka kada su kuskura su bude makarantun nasu, karya dokar da aka gindaya musu ka iya sawa rufe irin wannan makarantun na masu kunnen kashi.” In ji shi.