Harkokin kasuwanci sun dawo a Babbar Kasuwar Wuse da ke Abuja da kotu ta bude bayan cin tarar kungiyar ’yan kasuwar saboda saba dokar kariyar cutar COVID-19.
Kotun tafi-da-gidanka mai hukunta masu saba dokar kariyar cutar COVID-19 ta ba da izinin bude kasuwar ne kwana guda bayan ta ba da umarnin rufe ta.
Kotun karkashin jagorancin mai Shari’a Idayat Akande ta kuma ci tarar kungiyar ’yan kasuwar ta Wuse N50,000 kan saba dokar.
Sauran kasuwannin da kotun ta rufe tare da Kasuwar Wuse sannan ta yi masu afuwa bayan cin tarar su sun hada da cibiyar kasuwanci ta UTC, sai kuma Murg Shopping Mall, da dukkaninsu suka biya tarar da aka yi musu nan take.
Kwamitin Ministan Abuja na Tabbatar da bin dokar kariyar COVID-19, a karkashin jagorancin Shugabansa, Attah Ikharo, da shugabannin ’yan kasuwa da na jami’an tsaro, duk sun halarcin zaman shari’ar.
Kotun ta amsa buktar kungiyar ’yan kasuwar na neman a bude su ne bisa dalilan jinkai, bayan kungiyar ta dauki alkawarin tabbatar da bin dokokin kariyar cutar.
Sakataren Kungiyar ’yan kasuwar, Alhaji Abubakar Abdullahi ya ce tuni suka tanadi abubuwan wanke da na’urar auna zafin jiki da sunadaren wanke hannu tun daga kofofin kasuwar.
Ya ce an kuma tanadin hakan a shaguna, tare da tabbatar da cewa kowa ya sanya amawali da kuma bayar da tazara a tsakanin ’yan kasuwa da masu hulda da su.
‘’Yan kasuwa sun yi bore’
’Yan kasuwar da sauran masu hada-hada a kasuwar sun yi cincirindo a kan tituna da suka sada kasuwar a ranar Talata bayan rufe ta.
Wasu daga cikin matasa da lamarin ya ritsa da su da suka yi dafifi a kan titin da ke kusa da kasuwar, sun yi ta yin ihu tare da buga duk motar da ta nemi wucewa ta wajen.
Sun kuma rika korafin cewa ba su da komai a aljihunsu a lokacin da suka iso kasuwar suka same ta an rufe.
Daga bisani wasu daga cikin manyan ’yan kasuwar da taimakon jami’an tsaro sun samu nasarar shawo kan masu boren.
Aminiya ta samu labarin cewa yawancin ’yan kasuwar ba su samu bude shagunansu ba bayan bude ta a ranar ta Laraba.
Akasarinsu sun samu labarin umarnin bude kasuwar ne a lokacin da suke gida, sannan lokaci ya kure na su garzayo.