✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

COVID-19: Amokachi ya raba kayan tallafi a Kaduna

Tsohon dan wasan kwallon kafan Najeriya Daniel Amokachi ya raba wa talakawa kayan tallafi yayin da ake kullen coronavirus. Dubban mazauna Kaduna ne suka samu…

Tsohon dan wasan kwallon kafan Najeriya Daniel Amokachi ya raba wa talakawa kayan tallafi yayin da ake kullen coronavirus.

Dubban mazauna Kaduna ne suka samu tallafin kayar abincin da tsohon dan wan kungiyar Super Eagles din ya raba domin rage radin dokar kullen.

Akalla iyalai maza da mata 1,100 ne suka samu tallafin kayan abinci da sauran abubuwan bukatun da gidauniyar Amokachi ta raba.

Amokaci ya ce  gidauniyar ta fi ba wa mata kayan tallafin kasancewar su ne ke sarrafa kayan abinci a gida.

“‘Yar gudunmuwarta ke nan a lokacin nan na dokar kullen COVID-19,” inji tsohon da kungiyar Super Eagles din.

“Na kan taimaka wa talakawa sau hudu zuwa shida a shekara. Dama ce Allah Ya ba ni in taimaka wa mabukata kuma zan ci gabda da yin hakan matukar ina da hali.”

Amokachi dan asalin jihar Benue ya taso ne a Kaduna inda ya fara wasa a kungiyar kwallon kafa ta Ranchers Bees, kafin ya wakilci Najeriya a gasar cin kofin duniya sau biyu da kuma gasar Olympic.