Adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya kai 7,016, kamar yadda alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta NCDC na baya-bayan nan suka nuna.
Adadin ya kai haka ne dai bayan da aka samu sabbin majinyata 339 ranar Alhamis.
A cewar hukumar NCDC, 139 daga cikin sabbin majinyatan a jihar Legas suke, yayin da jihohin Kano da Oyo ke da mutum 28 ko wacce.
Sauran jihohin da aka samu sabbin kamu su ne Edo mai mutum 25, da Katsina mai 22, da Kaduna mai 18, da Jigawa mai 14, da kuma Yobe da Filato masu 13 ko wacce.
A Yankin Babban Birnin Tarayya kuma an samu karin mutum 11, takwas a jihar Gombe, biyar a Ogun, hurhudu a Bauchi da Nasarawa, uku a Delta, sai kuma Ribas da Adamawa masu mutum dai-dai.
Daga cikin jimillar mutum 7,016 da suka kamu zuwa yanzu dai an sallami 1,907 bayan sun warke, yayin da mutum 211 suka riga mu gidan gaskiya.
Hakan na nufin a yanzu akwai mutum 4,898 da ke jinya a fadin kasar.
Da wannan sabuwar kididdiga dai jimillar mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a jihar Legas ya kai 3,093 yayin da na Kano da na Yankin Babban Birnin Tarayya suka tashi 875 da 446 daki-daki.