✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

COVID-19: ‘Adadin gwajin da ake yi bai isa ba’

Adadin mutanen da ake yiwa gwajin cutar coronavirus a Najeriya bai wadatar ba, ana bukatar kari. Darakta Janar na Hukumar Bunkasa Kimiyyar Kananan Halittu ta…

Adadin mutanen da ake yiwa gwajin cutar coronavirus a Najeriya bai wadatar ba, ana bukatar kari.

Darakta Janar na Hukumar Bunkasa Kimiyyar Kananan Halittu ta Kasa (NABDA),  Farfesa Alex Akpa, ya fadi hakan a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Litinin a Abuja.

“Yawan mutanen da ake yiwa gwaji yanzu haka bai wadatar ba; don haka akwai bukatar a kara yawan mutanen da ake gwadawa a tabbatar da halin lafiyarsu”, inji Farfesa Akpa.

A cewar jami’in, wannan dalilin ne ma ya sa hukumarsa ta ba da gudunmawar dakunan bincikenta da ke Abuja da garin Odin a jihar Bayelsa don a rika amfani da su ana gwajin.

“Akwai bukatar a kara kaimi, shi ya sa ma muka bude kofofin wadannan dakunan binciken namu ko a samu Karin cibiyoyin gwaji a kasar nan”, inji shi.

Farfesa Akpa ya kuma ce dakunan binciken hukumar na da kayan na zamani, na gani na fada, wadanda ba a jima da kakkafa sub a, kuma za a iya amfani da su don gwajin COVID-19.

Jami’in ya kuma ce hukumar ta sarrafa man tsaftace hannu (wato sanitiser) don tallafawa a yakin da ake yi da annobar coronavirus.

“Shirin da muke yi shi ne sarrafa sanitiser har miliyan daya daga sinadarin bioethanol saboda amfanin al’ummar kasarmu, da nufin tallafa wa gwamnati ta kawo karshen wannan cuta mai hadari”.

A cewarsa an yi amfani da wani sinadari ne da ake samu a rogo da rake don sarrafa man don haka daukacin kayan da aka yi amfani da su a gida ake samunsu.

“Wannan sinadarin na bioethanol muke amfani da shi don sarrafa sanitiser dinmu kuma ingancinsa ya kai matakin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana, kuma za mu iya sarrafa da yawa don sayarwa”, a cewar Farfesa Akpa.

Farfesan ya kara da cewa za a iya samar da ayyukan yi da dama a arewacin Najeriya inda ake noman rake, da kuma kudancin Najeriya inda ake noman rogo.