Gwamnatin jihar Nasarawa ta kammala shirye-shiryen mayar da almajirai 4,443 zuwa jihohinsu na asali.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa za a kwashe almajiran, wadanda ba ‘yan asalin jihar ba ne, a mika su ga danginsu.
Majiyar ta kara da cewa gwamnatin ta gama shirya motocin da za su yi jigilar almajiran a ‘yan kwanaki masu zuwa.
- Almajirai 16 da aka mayar Kaduna daga Kano suna da Coronavirus
- Coronavirus: Jigawa ta karbi almajirai 524 daga Kano
- An kama malami mai almajirai 327 maza da mata a Kaduna
Gwamnatin za ta mayar da almajiran zuwa jihohi 19 da Yankin Babban Birnin Tarayya Abuja.
Almajirai 207 za a mayar jihar Adamawa, 701 Bauchi, 34 Binuwai, 24 Borno, 55 Gombe , 273 Jigawa, da kuma guda daya da za a kai jihar Enugu.
Sauran sun hada da 417 da za a kai Kaduna, 1,497 Kano, 689 Katsina, 208 Kebbi, 35 Kogi, 13 Kwara , 76 Niger, 3 Oyo, 160 Filato, 48 Sakkwato, 102 Taraba, 49 Yobe, 219 Zamfara da kuma daya da za a mayar Yankin Babban Birnin Tarayya.
A gefe guda kuma, almajirai 24,005 za a mayar wurin iyayensu a fadin jihar ta Nasarawa.
Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Ahmad Tijjani Aliyu, ya ce a wani taro da suka gudanar ta yanar gizo, gwamnonin jihohin arewacin Najeriya sun amince da mayar da almajirai zuwa jihohinsu na asali saboda su samu kulawar iyayensu.