Gwamnatin jihar Katsina ta soke dokar da ta dakatar da sallar Juma’a a fadin jihar.
Gwamnatin ta dage wannan dokar ne bayan wata tattaunawa da suka yi shugabannin addini da sarakuna da kuma jami’an tsaro a jihar.
Daukar wannan mataki dai na zuwa ne kwana guda bayan sanar da mutuwar wani likita a Daura, wanda ake kyautata zato coronavirus ce ta yi ajalinsa.
Da yake sanar da mutuwar ranar Talata, Gwamna Aminu Bello Masari ya ce ko da yake likitan ya rasu ne ranar Asabar sakamakon gwajin da aka yi masa bai fito ba sai bayan kwana uku.
Sakataren gwamnatin jihar Dakta Mustapha Inuwa ne ya bayyana dage dokar hana sallar Juma’ar a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, inda ya ce an dage dokar dakatar da sallar Juma’a ne nan take bayan ganawar da suka yi.
“Za a gudanar da sallar ta hanyar amfani da shawarwarin ma’aikatan lafiya da jami’an tsaro.”
A cewar Dakta Mustapha, Limaman masallatan za su gudanar da Sallar ne ba tare da tsawaitawa ba, don kammala ta cikin lokaci kadan.
An bukaci jama’a da su bar tazarar don rage cunkoso kamar yadda ma’aikatan lafiya suka sanar.