’Yan Majalissar Wakilan Tarayyar Najeriya sun sadaukar da albashinsu na watanni biyu domin yakar cutar Coronavirus a Najeriya.
Shugaban Majalissar, Femi Gbajabiamila, ya bayyana hakan a yayin da ya gudanar da sakon bidiyo ga ’yan Najeriya a ranar Talata.
Gbajabiamila, ya ce wannan mataki ne da muka dauka domin ganin an dakile cutar covid-19 a kasarnan.
“Mun hadu ne muka zartar da mu bayar da kashi dari (100%) na albashinmu na watanni biyu domin domin yaki da cutar covid -19 a Nijeriya.”
Wannan tallafi ya zo ne kwanaki kadan bayan Ministoci sun bayar da gudunmawar kashi 50 na albashinsu domin yaki da wannan annobar.
Idan muka waiwaiya, kwanaki kadan da suka gabata, Honarabul Mansur Manu Nasoro ya yi kira ga ’Yan majalisun da kowannensu ya tallafa da Naira miliyan daya domin ganin an shawo kan annobar Coronavirus a Najeriya.