’Yan uwan mutane hudu daga cikin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a jihar Bauchi sun ce da so samu ne da ba su yarda a killace ’yan uwan nasu ba.
Wasu daga cikinsu dai duk ba a bari a shiga inda ake killace wadanda suka kamu, sukan kewaya lokaci zuwa lokaci.
Danjuma Adamu Barde dan uwan daya ne daga cikin wadanda suke jinyar cutar, ya kuma shaida wa wakilin Aminiya cewa bindiga ce kawai ta raba su da dan uwansu saboda gwamnati ta kewaye wajen da aka killace shi ta ce ba wanda zai shiga.
“Muna son dan uwanmu yayanmu abin aklfaharinmu, wanda ginshiki ne a cikin danginmu; yaya ma za a ce mu guje shi [saboda ya kamu da coronavirus bayan] muna da yakinin ma zai warke?”
Shi ma Sama’ila Muhammed, wanda ya ce tun da ya tashi yake tare da yayansa wanda aka tabbatar ya kamu da cutar, don haka bai kamata ya guje a yanzu da wata larura ta same shi ba.
“Ko wanne irin ciwo ne ya same shi ba halacci ba ne mu guje shi; tun da doka ce ta ce a killace shi har Allah ya ba shi lafiya yanzu muna bin dokar.”
Muhammad ya kuma ce kafin a gano dan uwansa yana dauke da cutar ba wata alamarta a tattare da shi, amma gwajin da aka yi masa bisa umurnin likitoci saboda ya yi mu’amala da daya daga cikin wadanda aka tabbatar sun kamu ya nuna yana da ita.
“Shi bai ma yarda yana da cutar ba bayan da likitoci suka ce yana da ita, sai dai ya yi biyayya wa dokar hukumomin lafiya shi ya sa ya zauna a inda aka killace shi, kuma mu iyaslansa da ’yanuwansa da ya yi mu’amala da mu dukkanmu an dauki samfurin jininmu ba wanda aka samu yana dauke da cutar.
“Ko da ba za mu gan shi ba, nan asibiti muke yini muna yi masa addu’a Allah Ya fito da shi lafiya; da za mu guje shi da ba za ma muzo ba tun da mun san in mun zo ba za a bar mu mu shiga ba”
A cikin wadanda aka ce suna dauke da cutar a jihar Bauchi dai hukumomin lafiya sunan gwamnan jihar Bala Abdulkadir Muhammad kawai suka bayyana saboda abin da suka kira bin dokokin kula da lafiya, shi ma kuma shi ya amince a fada.
Wani mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum, Muhammad Jibril Sogiji, ya ce masu dauke da wannan ciwo ba abin kyama ba ne.
“Ka ga yanzu dai gwamnan Bauchi ya warke kuma har ma ya je ya yi sallar Juma’a a Babban Masallacin Bauchi da ke Kofar Fada ya kuma gaisa da jama’a ko da yake duk sun sanya abubuwan da suka rufe hanci da baki an kuma kamanta bin dokokin yin nesa da juna amma tare aka zauna aka yi mu’amala ba kyama ba tsangwama”, inji shi.
Sogiji ya kuma ce talauci kadai ya isa ya hana mutane gudun masu cutar tunda wadannan wadanda aka ce sun kamu da cutar mutane ne da Allah Ya sa abincin talakawa a hannunsu, don haka “ta yaya za su guje su? Ai dole su nuna kauna a gare su balle ma likitoci ba su ce cutar ba ta warkewa ba”.