✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Yadda MC Tagwaye ya ari bakin Buhari

Ina ‘yan Najeriyar da suke ta korafi a kan cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai ce komai ba game da cutar Coronavirus? Shahararren mai wasan barkwancin…

Ina ‘yan Najeriyar da suke ta korafi a kan cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai ce komai ba game da cutar Coronavirus?

Shahararren mai wasan barkwancin nan wanda kuma ya kware a wajen kwaikwayon Shugaban na Najeriya, MC Tagwaye, ya yunkura don ya debe muku kewa, ko da bai share muku hawaye ba.

MC Tagwaye dai ya fitar da wani jawabi a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis 19 ga Maris 2020 inda ya kwaikwayi Shugaban kasar – jawabin da ‘yan Najeriya suka yi ta dokin ji daga bakin shi Shugaba Buhari.

Kamar yadda MC Tagwaye  ya ce a cikin bidiyon inda ya yi shiga irin ta Buhari, “Ya ku ƴan Najeriya, ina yi maku magana ne ba a matsayin Shugaban Kasa ba kadai ba a’a, a matsayin dan-uwanku, kawun ku, sannan kuma a matsayin mahaifi.

“Ba sabon labari ba ne irin kalubalen da duniya take fuskanta, ciki kuwa har da Najeriya a kan wannan cuta ta Coronavirus (Covid-19) wadda ta zamo wata annoba da ke bukatar daukar tsatstsauran mataki na hana ci gaba da yaduwarta a duniya.

Wadannan matakai ba ana daukar su don kuntatawa wasu ba ne, a’a, ana daukar su domin tattabatar da cewa al’umma sun tsira daga kamuwa da ita.

Wannan gwamnati ba a bar ta a baya ba wajen ganin cewa tana daukar matakai domin yakar cutar.

Mun amince a gwamnatance da daukar wadɗannan matakai na gaggawa da suka hada da, 1. Dukkan jami’ai da ma’aikatan gwamnati, an hana su yin tafiya zuwa kasashen waje.

2. Daga cikin kokarin da muke yi na hana yaduwar Covid-19 mun hana ‘yan kasashen Amurka, Ingila, China, Japan, Iran, Switzerland, Norway, Netherlands, Faransa, Koriya ta rkudu, Jamus, Italiya da Spain shigowa Najeriya kamar yadda muka hana ‘yan Najeriya zuwa can.

3. Sannan an dakatar da bayar da iznin shiga, wato biza har sai abin da hali ya yi.

Wadannan su ne kalaman da MC Tagwaye ya yi a yayin da ya kwaikwayi Shugaba Buhari kamar yadda ya saba yi a baya.

https://twitter.com/mc_tagwaye/status/1240428544779522048