✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Coronavirus: Tottenham ta fice daga gasar Europa Conference

Tottenham ta caccaki hukuncin na UEFA wanda ta ce bai yi mata dadi ba.

Kungiyar Kwallon Kafa ta Tottenham ta yi asarar gurbinta a gasar UEFA Europa Conference (UECL) bayan da Hukumar Kwallon Kafar Turai UEFA ta yanke hukuncin cewa kungiyar ta yi asarar wasanta da Rennes da aka dage a baya.

Bayanai sun ce an dai dage wasa tsakanin Tottenham da Rennes na ranar 9 ga watan Disamba sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus da wasu ’yan wasan kungiyar ta Arewacin London suka yi.

Hakan dai na zuwa ne bayan da gwaji ya tabbatar ’yan wasanta 13 sun harbu da cutar, lamarin da ya sanya aka dage wasu wasanninta ciki har da na Firimiyar Ingila

Sai dai ahukuncin da ta yanke, hukumar UEFA  ta ce ba za a sake wasan ba, kana ta mika batun ga kwamitin da ke kula da dokokinta.

Kwamitin ya yanke hukuncin cewa an bai wa Rennes nasara 3-0, kuma ita ce ke kan gaba a rukunin nasu, Vitesse na biye, kana Tottenham ke matsayi na uku.

A wata sanarwa, Tottenham ta caccaki hukuncin na UEFA wanda ta ce bai yi mata dadi ba, sai dai ta ce ya zame mata dole ta karbi hakan, ta kuma mayar da hankali a kan sauran wasannin da suka rage mata a gasar da take ciki.

Kafofin Labarai na Turai sun ruwaito cewa, kocin kungiyar, Antonio Conte, ya ce ba za ta sabu ba domin kuwa an fara shirye-shiryen daukaka kara kan matakin na UEFA, inda za a maka hukumar a gaban kotun wasanni ta Court for Arbitration of Sports.