A ranar Asabar an samu karin mutum 3 da suka mutu a Najeriya sakamakon cutar Coronavirus a yayin da mutum 112 suka kasance sabbin kamuwa da cutar.
Hakan na kunshe ne cikin alkaluman da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa NCDC ta fitar kamar yadda ta saba duk rana.
- Za a fafata yakin basasa muddin aka kashe Gwamnan Binuwe – Wike
- Babu hannun Fulani a harin da aka kai wa Gwamnan Binuwai – Miyetti-Allah
Alkaluman sun nuna an samu karin mutum 45 da suka kamu a Legas, sai mutum 22 a Abuja Legas da kuma karin mutum 17 a Jihar Ondo.
A Jihar Ebonyi an samu mutum 9, sai Bauchi mai mutum 6 da kuma Jihar Kebbi mai mutum 4 yayin da aka samu mutum 2 a Delta.
Cikin sa’a 24 an samu karin mutum mutum 2 a Osun, da mutum 2 a Jigawa sai mutum daidai a jihohin Borno, Edo, Nasarawa da kuma Kano.
A jimilla yanzu, cutar Coronavirus ta harbi mutum 161,651 a fadin kasar tun bayan bullarta karon farko a watan Fabrairun 2020.
Kazalila, alkaluman na NCDC sun nuna cewa cutar ta kashe adadin mutum 1,487 yayin da an sallami mutum 147,775 bayan sun samu waraka sai kuma mutum 2,030 da suka riga mu gidan gaskiya kawo yanzu.